Kamar yadda ofishin yada labaran Hauza ya ruwaito, Ayatullah Sayyid Muhammad Sa'idi yau a taron Wurare Masu Tsarki a Jamhuriyar Musulunci ta Iran na takwas, wanda aka gudanar a Masallacin Jamkaran, ya bayyana cewa: Matsayin wuraren masu tsarki a lokuta daban-daban a tarihi, ya kasance daidai da yanayin lokaci da abubuwa da suke faruwa a duniyar Musulunci, kuma dama jama'a ko yaushe abin da suke tsammani kenan.
Yana mai cewa, Ahlul Bayt (A.S) a kowane zamani suna yin bayani daidai da bukatun al'umma, hali da matsayi yayin isar da saƙon su na musamman, ya kara da cewa: A yau ma wurare masu tsarki dole ne su kasance da matsayi mai ma'ana, bayyananne kuma na zamani; musamman a cikin al'amuran da ke faruwa a fagen duniyar Musulunci ko kuma abubuwan da zasu iya haifar da tasiri a tunanikan jama'a.
Ayatullah Sa'idi, da yake nuni da rawar da Sayyida Fatima Ma'suma (S.A) ta taka a Qum da tasirin kasancewarta a wajen samuwar babban makarantar ilimin addini (Hauza), ya bayyana cewa: Bisa ga sahihan riwayoyi, wannan babbar Uwargida tun ma kafin ta kammala balaga, tana ba da amsoshin tambayoyin fikihu da aƙida na jama'a kuma wannan yana nuna ingantacciyar tarbiyyarta ta ilimi a cikin Imamai masu tsarki (A.S).
Ya kara da cewa: Hijirar Sayyida Ma'suma (S.A), kokari da kuma kasancewarta a Qum, sun sa wannan birni a hankali yana zama gidan Ahlul Bayt (A.S), wanda bayan barazanonin da suka faru a lokuta daban-daban ga Hauzar Najaf, a yau Qum ita ce babbar Hauzar Ilmin Shi'a kuma tushen juyin juya halin Musulunci.
Shugaban Haramin na Sayyida Ma'asuma (S.A) ya bayyana cewa ɗaya daga cikin muhimman ayyukan masu mas'uliyya shi ne su fayyace wannan tarihin mai kyau, wato matsayi da wayewar Qum, kuma ya bayyana cewa: Matan wannan zamanin dole ne su sani cewa Ahlul Bayt (S.A) tare da kiyaye kawaici da hijabi, su ne ainihin ababen koyi a rayuwar addini.
Shugaban Haramin Sayyida Ma'asuma (S.A) a ƙarshe ya ankarar cewa: Haramin Ahlul Bayt (A.S) yana tsare tunani da ruhin jama'a, don haka kuma dole ne a kiyaye shi cikin lura, hikima da girmamawa.
Your Comment